Kungiyar Tsoffin Shugabannin Kananan Hukumomin Jigawa karkashin jam’iyyar PDP a zamanin tshohon Gwamnan jihar, Sule Lamido sun yi kira ga Mustapha Sule Lamido, Santuraki, da ya fito ya nemi takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023.
Kungiyar ta gudanar da taron kiran ne a ranar Litinin a dakin taro na Masarautar Gumel da ke garin Gumel a jihar Jigawa.
Sakataren Kungiyar Gwamnonin kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Yankwashi, Musa Abdullahi Karkarna ne ya sanar da manema labarai kiran da sukai ga Santurakin.
Ya baiyana cewa, sun yi wannan kiran ne saboda irin cancantar da Santurakin yake da ita da kuma fatan zai yi irin mulkin mahaifinsa tsohon Gwamna Sule Lamido a jihar.
Musa Abdullahi ya kara da cewa, wannan kira nasu ba yana nufin sauran masu sha’awar takarar gwamna a jam’iyyar PDP kar su fito ba, sai dai yana nuna su tsofin ciyamomin suna nuna goyon bayansu a kan Mustapha Sule Lamido sama da saura.
Ya kara da cewa, kungiyar ta su za ta goyi bayan duk wadda jam’iyyar PDP ta fitar a karshe a matsayin dan takarar gwamna a jihar Jigawa.