For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsohon Rijistaran NECO Ya Zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University

Tsohon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa, NECO, Farfesa Abdulrashid Garba ya zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University, KHAIRUN, na farko.

KHAIRUN dai na ɗaya daga cikin sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Kano da suka sami lasisi, sannan an saka mata sunan wanda ya samar da ita, sanannen ɗan kasuwa kuma malamin Musulunci, Khalifa Isyaka Rabiu.

A takardar da ya rabawa manema labarai, Sakataren Gudanarwa na Jami’ar, Malam Yusuf Datti ya ce, naɗin Farfesa Garba wanda ƙwararre ne a fannin bayar da shawarwari da nusarwa kan ilimi, ya samu amincewar Kwamitin Amintattu na Jami’ar ƙarƙashin jagorancin Babban Farfesa, Muhammad Sani Zahraddeen.

Farfesa Garba dai yana da ƙwarewar koyarwa ta kimanin shekaru 33, sannan kuma ya taɓa zama Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Kano da kuma Mai Bayar da Shawara na Musamman ga Ministan Ilimi da kuma zama Shugaban Hukumar NECO.

Comments
Loading...