For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsohon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano, Rimin-Gado Ya Koma PDP

Dakataccen Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Barrister Muhyi Magaji Rimin-Gado ya koma jam’iyyar PDP ana daf da fara shiga yakin neman zaben 2023.

Rimin-Gado ya fadawa jaridar yanar gizo ta Kano Focus cewa, ya cike bukatar shiga PDP ta hanyar yanar gizo yayin da kuma yake shirin yin rijistar a mazabarsa da ke karamar hukumar Rimin-Gado a watan Fabarairu mai zuwa.

Tun bayan dakatar da shi da gwamnatin Kano ta yi a ranar 5 ga July, 2021, hotunan tsohon shugaban suke ta zagaya Kano ana nuna yana takarar gwamnan Kano a 2023.

Wadansu hotunan ba sa dauke da alamar jam’iyya yayin da wasu kuma suke dauke da alamar jam’iyyar APC.

Haka kuma an gano cewa, Rimin-Gado ya kauracewa al’amuran da suka shafi jam’iyyar APC a matakin karamar hukuma da kuma jiha, sannan kuma ba a ji shi a wani bangare daga bangarori biyu masu rigima kan shugabancin APC ba.

Idan za a iya tunawa a baya a watan Disamba na 2021, ‘yansanda sun dakatar da taron da aka shirya wanda Rimin-Gado zai yi jawabi ga dubunnan matasa a matsayin ranar tunawa da yaki da cin hanci da rashawa ta duniya, inda ‘yansanda suka rufe dakin taron.

Da yake jawabi kan dalilinsa na shiga jam’iyyar PDP, Rimin-Gado ya ce, ya shiga PDP ne saboda ita kadai ce jam’iyyar da ta rage wadda za ta iya ceton Kano daga rikicin siyasar da ake ciki.

Rimin-Gado ya kara da cewa, PDP a matsayin daidaitacciyar jam’iyya za ta tsarkake Kano daga rikice-rikicen siyasa a shekarar 2023.

“Na yi nazarin yanayin siyasar Kano da ake ciki a halin yanzu kuma na gano cewa da wannan rigingimun cikin gida da ke tsagin Ganduje da na Shekarau a APC, PDP ce kadai mafitar da za ta iya magance matsalolin.

“Matsalar waye zai zama gwamna a gaba, ko su waye za su zama ‘yan Majalissar Dattawa a mazabu uku ba sune ya kamata mu sa a gabanmu ba, abin da ya kamata mu yi, shine yanda za a fitar da Kano daga yanayin rikicin siyasar da take ciki. Siyasa ba harkar ko a mutu ko ai rai ba ce.

“Na shiga PDP domin na yiwa mutane na da jiha ta hidima. Na yi haka a lokacin Gwamnatin APC kuma na yi shirin kara bayar da gudummawa a kowacce jam’iyya na ke,” in ji shi.

(PUNCH)

Comments
Loading...