Tunisia ta fitar da Najeriya daga gasar cin kofin Afirka a Kamaru, inda ta samu sa’ar Super Eagles da ci 1 – 0.
Tunisia yanzu za ta hadu da Burkina Faso a kwata fainal.
Najeriya ta buga kusan rabin wasan ne da mutum 10 bayan Alex Iwobi ya karbi jan kati.
Dan wasan Youssef Msakni ne ya ci wa Tunisia kwallonta a raga, minti biyu da dawowa hutun rabin lokaci.
Sakamakon ya bada mamaki ganin yadda Najeriya ita ce kasar da ta ci dukkanin wasanninta uku a zagayen farko, kuma wadda korona ba ta yi wa illa ba.
Tunisia wacce ta lashe kofin a 2004, a ranar Asabar za ta hadu da Burkina Faso, 29 ga watan Janairu.
(BBC Hausa)