Mai Tsawatarwa a Majalissar Dattawa, Sanata Orji Uzor-Kalu, ya taya jam’iyyar PDP murnar zaɓar Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa a babban zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, Kalu ya ce, samun nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani na PDP ya nuna cewa ƴan Najeriya sun fahimci lissafin siyasarsa kan shekarar 2023.
Ya yi kira cewa, tun da Atiku ya fito ne daga yankin Arewa maso Gabas, ya kamata jam’iyyar APC ita ma ta miƙa takarar Shugaban Ƙasa zuwa yankin.
Kalu ya ce, “Na taya PDP murnar zaɓar ɗan yankin Arewa maso Gabas a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa. Da alama ƴan Najeriya sun fahimci abun da na fahimta jiya.
“Game da jam’iyyarmu APC, yanzu babu mafita a cigaba da tattaunawa kan miƙa kujerar Shugaban Ƙasa zuwa Kudu sai dai in APC ta shirya yiwa kanta ritaya ne a siyasa.
“A duk wani tsarin demokaraɗiyya, shugabannin ƙasashe da gwamnoni suna nuna goyonbaya da kuma zaɓar waɗanda zasu gaje su. Ina kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya zaɓi magajinsa daga yankin Arewa maso Gabas, wannan shine daidaiton da yankin Kudu maso Gabas ke buƙata. Idan Arewa maso Gabas ta samu, to an kusa kammala zagaye yankuna wajen fitar da Shugaban Ƙasar Najeriya.
“Zuwa yanzu ya kamata dukkanin ƴan takara a APC su janye tare da goyawa ɗan Arewa maso Gabas baya. Sanata Ahmad Lawan ne mafita.
“Ina taya ƴan Arewa maso Gabas murna a daidai lokacin da muke jiran samun Shugaban Ƙasa daga Arewa maso Gabas.”