For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Waɗanda Ruwa Ya Cinye A Maiduguri Na Zanga-Zanga Kan Rashin Abinci Da Tallafi

Daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri, Jihar Borno, sun yi zanga-zanga yau kan rashin abinci da kayan tallafi bayan ambaliyar da ta auku ranar 9 ga Satumba, 2024.

Ambaliyar ta raba sama da mutum miliyan ɗaya da gidajensu tare da lalata muhimman gine-gine, inda da dama suka rasa damar samun abubuwan gudanar da rayuwa.

Masu zanga-zangar, yawancinsu daga unguwar Baga Road, sun toshe hanyoyi don nuna fushinsu game da rashin kulawa da samun tallafin.

Kwamishinan Ƴan Sanda, CP na Jihar Borno, Mohammed Lawal Yusufu, ya yi kira ga mutanen da su kwantar da hankalinsu, yana tabbatar musu da cewa gwamnatin Jihar Borno tare da hukumomin NEMA da SEMA sun kaddamar da shirye-shiryen raba taimakon tallafin da aka samu.

Ya kuma gargade su da su kauce wa toshe hanyoyi domin kada a sami cikas wajen isar musu da tallafin.

An rawaito cewa, an fara rabon kati ga wadanda suka rasa muhallansu domin karɓar tallafin abinci daga gwamnati.

Gwamnatin Jihar Borno da kungiyoyin agaji suna aiki tare don samar da abinci, muhalli, da ruwan sha mai tsafta, yayin da ake ci gaba da kokarin kwashe mutum 50,000 zuwa wuraren zama na wucin gadi.

Ambaliyar ta shafi fiye da mutane 239,000 a Maiduguri, tana kuma haifar da barazanar yaduwar cututtuka musamman a sansanonin ƴan gudun hijirar.

Comments
Loading...