Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma, WAEC, ta saki sakamakon jarabawar kammala babbar sikandire ta shekarar 2022.
Da yake jawabi a yau Litinin a ofishin WAEC na Yaba, Shugaban Ofishin Hukumar na Najeriya, Mr. Patrick Areghan ya ce, “An dora sakamakon a shafinta na yanar gizo. Daliban da suka rubutawar kuma suka cika sharudan biyan kudadensu ga hukumar zasu iya fara duba sakamakon jarabawarsu cikin awanni 12 masu zuwa.
“Za a tura kwafin sakamakon jarabawar ga makarantu nan ba da jimawa ba. Ba sai na jaddada ba cewar, sakamakon jarabawar wadanda jihohinsu ke biya musu, kuma hukumar WAEC ke bin jihohin bashi, ba zai fit aba har jihohin sun biya abun da ake bin su. Muna kira gare su da su biya domin samawa daliban damar duba sakamakon jarabawarsu.”
Ya kara da cewa, wadansu makarantu ba su dora sakamakon CA a manhajar da ake dorawa ba a kan lokacin da ya dace, haka kuma da yawa sun gaza yin rijista a kan lokaci, abun da ya jawo wasu makarantun ba su iya gabatar da dalibansu wajen rubuta jarabawar ba.