Rabbi Allah Ar-Rahimu
Rabbi Kai ne Rãhiminmu
Rabbi Kai ne Khãliƙinmu
Mai yawan jin ƙai gare mu
Yau fa ga Bãba gare mu
Har ila yau mãlaminmu
Yai wafati ba da jinkiri ba.
Dakta Ahmad Mãlami ne
Mãlamin mutafannini ne
Gun karãtu mã gwani ne
Har wa yau shi hãziƙi ne
Gã shi har yau jãrumi ne
Gun hadisi ma daban ne
Bai zamo mai ji da kai ba.
Rãyuwarsa gaba ɗayanta
In ka lura gaba ɗayanta
Bãbu wasa duk cikinta
Bãbu komai duk cikinta
Sai karãtu fal cikinta
Sai karantarwa cikinta
Bai zamo mai ɓãta lõkaci ba.
Ɗãlibansa idan ka gan su
Ko ka zauna nan gabansu
Ko ka saurara wajensu
Zã ka san ilimi a gunsu
Har da tarbiyya wajensu
Har tawãdu’u ma wajensu
Bã su zam aiki na hantara ba.
Rabbi Allah Yai hukunci
Duk da cewa mun yi ƙunci
Don rashin sarkin karamci
Malami mai son zumunci
Gã shi mai hikimar azanci
Gã shi mai tsabar mutunci
Bai zamo kyara ga ɗan Adam ba.
In kana zancen adãla
Mãlami ne mai adãla
In kana zancen kamãla
Mãlami ne mai kamãla
Gã shi bai wasa da salla
In ka tare duk jimilla
Ɗan Adam yake ba mala’ika ba.
Mãlami ne bã ɗagãwa
Mãlami mai son tilãwa
Gã shi bã yã yin adãwa
Gã shi mai ƙarfin tilãwa
Gã shi mai son taimakãwa
Malamin nan nai yabãwa
Gaskiya bã zan ƙi in faɗã ba.
Mãlami ne ba gadãra
Gã shi bã yã yin tijãra
Bã tsimi yau bã dabãra
In ka gan shi a kan kujera
To karãtu zã ya rera
Ko bayãni zã ya jera
Zã ya yo bã tãre da gardama ba.
In ana zance na sunnah
Mãlami ne shi na sunnah
Mai karantarwa ta sunnah
Gã shi jãgora a sunnah
Gã shi mai kishi na sunnah
Gã shi mai son yãɗa sunnah
Bai zamo bidi’a ga al’uma ba.
Littafan nan duk na sunnah
Har Bukhãrin nan na sunnah
Har da Muslim mã na sunnah
Har Abu Dauda na sunnah
Tirmizin mã dai na sunnah
Dãrumin nan mã na sunnah
Bãbu wanda fa bai biya wa al’uma ba.
Wanga mutuwa tã yi dūka
‘Yan Kano yau mun yi kūka
Ɗalibai duk mun yi kūka
Mãlamai mã sun yi kūka
Mãsu mulki sun yi kūka
Tãjirai ma sun yi kūka
Don rashin mãlaminmu babba.
Rabbana nã zõ gare Ka
Saifu ne bãwa gare Ka
Rabbi nai rõƙõ gare Ka
Nã yi rõƙõ dai gare Ka
Addu’ãta yau gare Ka
Gafara da tarahhuminKa
Kai masa bã tãre da sun tsaya ba.