Duk da karbar wani bangare na kudin fansa naira miliyan 6, wadanda sukai garkuwa da yarinya ‘yar shekara 5, ‘yar jihar Kano, Hanifa Abubakar, sun kashe ta.
Kawun Hanifa Abubakar, Suraj Suleiman, ya tabbatar da kisan da kuma gano sassan jikinta a Mushroom Private School da ke Tudunwada a Kano.
Ya bayyana cewa, wanda yai garkuwa da ita da farko ya dauketa zuwa wajen matarsa, amma matar ta ki karbarta.
“Mai garkuwa da ita, da farko ya kai ta wajen matarsa amma matar ta ki karbarta. Sai ya kaita Tudunwada inda yake da makarantar kudi, ya sanyawa shayinta kashin bera,” in ji kawun nata.
KU KARANTA: Sojoji Sun Kubutar Da Mutum 8 Da Akai Garkuwa Da Su Tare Da Kashe ‘Yan Ta’adda 3
“Bayan ya sanya mata gubar ta mutu, wanda yai garkuwa da itan sai ya daddatsata gunduwa-gunduwa ya binneta a makarantar.”
Jaridar DAILY NIGERIAN ta gano cewa, an kama wanda yai garkuwa da Hanifa Abubakar ne a wajen Titin Zaria a Kano a daren jiya lokacin da yake kokarin karbar cikon kudin fansar.
An yi garkuwa da yarinyar ‘yar shekara 5 ne a ranar 4 ga Disamba na shekarar 2021.