For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Abin Fashewa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 32 Da Jikkatar 53 A Afganistan

Akalla mutane 32 ne suka mutu, 53 kuma suka raunata a wani masallacin ‘Yan Shi’a da ke Afganistan sakamakon fashewar wani abu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya fitar da labarin, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar nan a wani masallacin ‘Yan Shi’a da ke birnin Kandahar.

Wani likita da ke aiki a babban asibitin birnin Kandahar, ya shaidawa AFP cewa, an kai gawarwaki 32 da kuma wadanda suka jikkata 53 zuwa asibitinsu.

Ba a dai tantance takaimaimai abin da ya jawo fashewar ba, sai dai lamarin ya faru ne mako guda bayan wani harin nab akin wake da aka kaiwa ‘Yan Shi’ar a birnin Kunduz da ke Arewacin Afganistan.

Harin da wani rukuni na kungiyar IS ta dau alhakin kaiwa.

Wani wanda harin Juma’ar nan ya faru a idonsa, ya shaidawa AFP cewa, ya ji karar fashewar abubuwa uku ne, daya a babbar kofar masallacin, wani a kofar barin Kudu na masallacin da kuma wani a inda mutane suke alwala.

Comments
Loading...