Wani tsohon ma’aikacin ofishin kula da manhajar biyan albashi ta IPPIS a Hukumar Raba Dai-dai ta Gwamnatin Tarayya, FCC, Haruna Kolo, wanda aka zarga da karɓar cin hanci kafin ya bayar da aiki, ya amsa laifinsa.
Ya amsa cewar, ya karɓi kuɗin da yawansu ya kai naira miliyan 75 daga masu buƙatar aiki a bisa umarnin shugabar ma’aikatar.
Kolo ya ce, Shugabar FCC ce ta umarce shi da ya sa kuɗin a asusunsa na banki sannan daga baya ya cire ya kai mata tsabarsu gidanta, abin da ya ce ya yi hakan a lokuta da dama.

Kolo dai na yin wanna jawabi ne a lokacin bincike kan rashin amfani IPPIS kan ƙa’ida da Kwamitin Majalissar Wakilai ke yi a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.
Da yake mayar da martani kan maganganun Kolo, shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa wajen tono gaskiya tare da bayyana ta ga ƴan Najeriya.
Ya ce, kwamitinsu ba zai zauna haka kawai yana ganin ana ɓarnatar da dukiyoyin al’umma ba tare da ya yi komai ba.
Kwamitin ya buƙaci Kolo da ya gabatar da shaidu kan abubuwan da ya faɗa, sannan ya ɗage ci gaba da sauraron lamarin zuwa yau Talata.