Daga: BBC Hausa
Kungiyar ci gaban al’umar Gobirawan Najeriya ta rubuta wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wata budaddiyar wasika wadda take neman ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a arewacin kasar.
Wasikar ta zayyano dimbin matsalolin da yankin ke fama da su da kuma wasu hanyoyi da suke ganin idan an bi, za a iya magance wadannan matsaloli.
Budaddiyar wasikar da kungiyar ci gaban al’umar Gobirawa ta rubuta wa Shugaba Buhari, ta fara ne da nuna damuwa kan kashe-kashen mutanen da ake yi ba tare da daukar mataki ba – musamman a kananan hukumomin Sabon Birni da Goronyo da Isa da kuma Shinkafi da ke jihohin Sokoto da Zamfara.
Kungiyar ta ce wadannan kananan hukumomi na fama da hare-hare daga wasu manyan ‘yan bindiga irinsu Bello Turji da yaransa wadanda ke cin karensu babu babbaka a yankin.
Sun ce ‘yan bindigan na kashe wanda suka so a lokacin da suke so da kuma yin karfa-karfa ta hanyar karbar haraji da kwace abincin mutane da magunguna.
Wasikar ta kara da cewa wadannan mutane sun zama tamkar wata gwamnti, ta yadda suke cire shugabannin al’umma su nada nasu da suke so.
Wasikar ta kara da cewa babu isassun dakarun tsaro a yankin, duk lokacin da suke kai dauki irin na fargar jaji ne, kuma basa iya cimma wadannan mahara a lokuta da dama.
‘Dan Ta’adda Ne Ke Mulkin Yankinmu’
Alhaji Ibrahim Alhasan shi ne shugaban ƙungiyar, kuma yi wa BBC karin bayani kan dalilin da ya sa suka rubuta wasikar a daidai wannan lokaci:
“Yau halin da jama’armu ke ciki ya ta’azzara, kasarmu ma ba gwamnatin Najeriya ce ke iko da ita ba, wani dan ta’adda ne ke iko da ita.”
BBC: Me kake nufi da wannan maganar?
Ibrahim Alhassan: Shi ke da hakimai. Ya nada hakimai a garuruwa, kuma shi ke zartar da hukunci, domin duk abin da za a yi sai da sanin shi.
BBC: A wace kasa ke nan ka ke nufin wannan lamarin ke faruwa?
Ibrahim Alhassan: Sabon Birnin Gobir.
BBC: Wane ne iko da garin tun da ka ce ba gwamnati ce ba?
Ibrahim Alhassan: Wani dan ta’adda mai suna Bello Turji wanda shi ke bi garuruwa yana aza haraji, yana kuma nada hakiman da ya ga dama. Ai shi ke da iko. Bau hukuma, sai abin da y aga dama yake yi. Ya kashe wannan yau, kuma yayi duk ta’asar da ga dama.
BBC: Wani zai iya tambayarku me yasa sai yanzu ku ka rubuta wa Shugaba Buhari wannan budaddiyar wasikar?
Ibrahim Alhassan: Kwanan nan an kashe mutane a Illela da Goronyo da Garki da Lalle a kasar Sabon Birni. Ranar Litinin mutane sun taso daga Sabon Birni za su Gusau cikin mota, ‘yan ta’adda su ka tare su kuma suka kashe su sannan suka cinna wa motar wuta. Mutanen nan su wajen arba’in da wani abu. To ai abin ya kai inda ya kai.
‘Lamarin ya Wuce Duk Inda Ake Tsammani’
Shugaban kungiyar Gobirawan Ibrahim Alhassan ya koka kan yadda lamarin rashin tsaro ya tabarbare.
Ya ce a halin yanzu kusan babu wani aikin gina kasa da ake yi:
“Babu noma, babu tafiya kumababu kasuwa. Babban tashin hankalin da muke fuskanta a yau shi ne kana cikin gidanka sai ‘yan ta’adda su zo su tozarta ka gaban iyalinka. A tara iyalanmu a yi fasikanci da su. A debi wasu jama’ar a tafi da su kuma a ce sai ka biya kudin fansa.Kuma duk garuruwan da na gaya maka, babu garin da aba a aza ma haraji ba, kuma sun biya. Amma duk da sun biya, basu sami zaman lafiya ba.”
Wannan kungiya ta Gobirwa ta ce ta aikewa shugaban Najeriya kwatankwacin irin wannan wasika a kwanakin baya, lokacin da aka kai wani hari a kauyen Garki mai nisan kilomita biyar tsakaninsa da Sabon Birni, inda aka kashe sama da mutum 80 a cikin dare guda.
Kauyuka irin su Gajit da Lajinge da Tarah da Unguwar Lalle da Kurawa da Gangara da Garin Idi da sauransu duk sun saba da hare-haren da wadannan ‘yan bindiga ke kai mu su, ta yadda suke kone garuruwansu da kuma amshe gonakinsu.
Wannan na zuwa ne bayan wani hari da sojojin Najeriya suka kai kan ‘yan bindigar wadanda daga baya suka gudu suka mamaye wadannan kauyuka.