
Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya sanar da karin albashi ga ma’aikatan jihar na kaso 10 cikin 100, wanda zai fara a watan Janairu na 2023.
Gwamnan ya sanar da matakin ne a bikin Ranar Aikin Gwamnati ta Shekarar 2022 wadda aka gabatar a Sakatariyar Gwamnatin Jiha ta Jerome Udoji da ke Awka.
Ya kuma sanar da shirinsa na bayar da naira 15,000 ga kowanne ma’aikacin jihar a kowanne mataki a matsayin tukuicin Kirsimeti domin siyan kayan abinci ga iyalai.
A cikin abubuwa biyar da gwamnatin Soludo ta sanya a gaba, ya tabbatar da cewa jihar ba ta fada cikin tarkon batagari ba, ta hanhyar fitar da su daga jihar, da kuma rusa aiyukansu, ciki har da dokar zaman gida wadda ta durkusar da aikin gwamnati da tattalin arzikin jihar.