Wani Kirista da aka baiyana cewa dan asalin jihar Cross River ne ya canja addininsa saboda kallon shirin Hausa mai dogon zango mai suna Izzar So.
Mai shirya shirin kuma jarumi a cikin shirin, Lawan M Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Instagram a ranar Asabar da ta gabata.
Lawan ya baiyana cewa, Kiristan wanda asalin sunansa shine John yanzu ya koma Umar bayan ya yi tattaki zuwa Kano tare da karbar kalmar shahada.
Lawan ya rubuta: “Masha Allah a yaune muka yi babban kamu a Musulunci, inda wannan bawan Allah ya shiga Musulunci saboda kallon IZZAR SO da yake yi, tun daga Cross River, Idom Ikon Local Government, Cross River. Yanzu haka dai ya karbi Musulunci, kuma yanzu haka sunansa ya koma Umar daga John. Muna yi masa addu’ar Allah Ya sa ya shigo addinin Musulunci a sa’a, Allah Ya sa ya amfane shi, amin.