For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Likitan Gargajiya Ya Rataye Kansa A Jihar Benue

Al’ummar mazabar kansila ta Mbakuha da ke karamar hukumar Ushongo ta Jihar Benue sun tsinci kansu cikin rudani bayan wani likitan gargajiya dan garin ya kashe kansa ta hanyar rataya.

Likitan da aka baiyna sunansa da Terhemen Iorbee, a baya dai an baiyna batansa kafin daga bisani a gano gawarsa a rataye a jikin bishiya.

Al’amarin da ya faru a cikin kwanakin karshen makon nan, ya sanya mutanen garin cikin rudani.

Duk da ba a samu wani rubutu da ke baiyana dalilin kashe kan ba, mutanen garin sun bayyana cewa, a ‘yan kwanakin nan likitan ya nuna bakin halaye.

“Babu wani abu da zai nuna dalilin aikata kisan kan, sai dai ‘yan bakin halaye da yake nunawa ‘yan satannin nan.

“Likitan gargajiya ne kuma yana auren mata uku yana kuma da ‘ya’ya hudu,” in ji daya daga cikin mazauna garin.

Lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan Jihar Benue, Catherine Anene, ta tabbatar da rataye kan da likitan ya yi.

(PUNCH)

Comments
Loading...