For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Ma’aikaci Ya  Mayarwa Gwamnatin Jigawa Maƙudan Kuɗaɗen Da Akai Masa Aringizo A Albashinsa

Wani ma’aikacin Gwamnatin Jihar Jigawa da ke aiki a jami’ar jihar ta Sule Lamido University da ke Kafin Hausa, ya mayar da kuɗi kimanin naira dubu ɗari takwas da sittin da takwas da ɗari bakwai da saba’in da bakwai da kwabo tamanin da tara (N868,777.89) ga gwamnatin jihar bayan kuskuren yi masa aringizo a yayin biyansa albashi.

Ma’aikacin mai suna Isma’il Salisu Bature, ɗan asalin garin Jahun ne a Jihar Jigawa, kuma yana aiki da sashin yaɗan labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar.

A ranar Talata, 25 ga watan Yuli ne dai gwamnatin Jihar Jigawa ta biya ma’aikatan jihar albashin watan Yuli kamar yanda ta saba tsawon lokaci.

Sai dai a lokacin da ya ji ƙarar faɗowar albashin nasa, bisa mamaki sai ya ga kuɗaɗen da suka haura abin da aka saba biyansa duk wata a matsayin albashi.

Labari Mai Alaƙa: Ƙara Kuɗin Makaranta; Anya Kuwa Ba A Tsokano Wata Fitinar Ba?

Wannan lamari ya sanya Isma’il garzayawa sashin biyan albashi na jami’ar domin sun warware masa bayani kan abun da ke faruwa, a kuma ba shi damar mayarwa gwamnati kuɗin da ba nasa ba.

Ismai’l ya shaidawa TASKAR YANCI cewa, ya samu nasarar mayar da kuɗaɗen da ba na sa ba cikin asusun gwamnati bayan sashen albashin jami’ar ya tantance masa albashin nasa.

Isma’il ya kuma yi kira ga al’umma su yi koyi da halin riƙon gaskiya da amana da nuna rashin zarmiya, domin a cewarsa, ta haka ne kaɗai al’umma zata ci gaba a kuma samu zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi.

Jama’a da dama da suka sami wannan labarin, na ci gaba da yabawa Isma’il Salisu Bature da aka fi sani da Bature Jahun kan halin gaskiya da riƙon amanar da ya nuna.

Comments
Loading...