Wani magoyin bayan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ya faɗi ya mutu a lokacin Babban Taron Zaɓen Shugabannin Jam’iyyar na ranar Asabar.
Magoyin bayan na kan hanyarsa ne ta zuwa filin taron Eagle Square lokacin da ya faɗi ya mutu.
Ɗaya daga cikin waɗanda ke tare da shi ya ce, marigayin da farko ya yi ƙorafin yana jin hajijiya daga bisani kuma ya faɗi.
Wakilin DAILY TRUST a wajen da abun ya faru ya gano cewa, magoya bayan jam’iyyar da dama ne sukai ƙoƙarin temakonsa amma ba su samu nasara ba.
Daga bisani an lulluɓe mamacin inda wasu mutane haɗin gwiwa jami’an tsaro suka ɗauke shi daga wajen.
(DAILY TRUST)