Wani malamin makarantar Royal Science Academy School mai suna Sirajo Ahmed dan shekaru 25 an cafke shi da zargin cin zarafin yarinya ‘yar shekara bakwai.
An zargi Sirajo da aikata laifin ne a ofishinsa da ke makarantar da Alkaleri na Karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da lamarin a jiya Talata, inda ya kara da cewa, bayan an kama Sirajo ya amsa laifinsa.
Ahmed ya ce, “Da misalin karfe 9:30 na safiyar 6 ga watan Satumba, 2022, jami’an bincike da ke ofishin ‘yansanda na Alkaleri, sun kama wani da ake kira da Sirajo Ahmed, mai shekaru 25, na makarantar Royal Science Academy, Alkaleri, da laifin cin zarafin dalibarsa ‘yar shekara 7.
“Labarin da aka samu a ofishin ‘yansandan ya nuna cewa, a ranar 13 ga watan Agusta, 2022, da misalin karfe 10 na safe, Ahmed dan Unguwar Ajiya Alkaleri, wanda malamin makaranta a ne a Royal Science Academy, Alkaleri, cikin yaudara ya ja dalibarsa ‘yar shekara bakwai zuwa ofishinsa da ke makarantar inda yai lalata da ita. A lokacin bincike, wanda ake zargin ya masa laifinsa.”