Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta kama wani mutum ɗan shekara 50 mai suna Ibrahim Adamu da gangancin yin amfani da abu mai kaifi wajen yanka agolan gidansa ɗan shekara huɗu a duniya.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da TASKAR YANCI ta samu.
Ya ce, lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Dinya da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa.
Sanarwar ta ce, jami’an ƴansandan sun samu labarin faruwar lamarin ne a ranar 8 ga watan Agustan nan da misalin ƙarfe 9:30 na dare, inda aka sanar da su cewar an ga gawar yaro ɗan shekara huɗu mai suna Salmanu Umar kwance a cikin jini da wawakeken yanka a maƙwagoronsa.
KARANTA WANNAN: Wani Tsoho Ɗan Shekara 84 Ya Kashe Matarsa Saboda Ta Ƙi Kwanciya Da Shi
Da samun labarin ne ƴansandan da ke ofishin ƴansanda na Roni, suka garzaya wajen, inda suka kai yaron Babban Asibitin Kazaure, wanda a can ya cika.
DSP Shiisu ya ce, bayan an yi bincike, an kama wani mutum ɗan shekara 50 mai suna Ibrahim Adamu ɗan ƙauyen Unguwar Dinya a ƙaramar hukumar, wanda aka gano cewar mijin babar yaron ne.
Jami’in ya ce, da aka tuhumi wanda ake zargin ya amsa laifin, inda ya ce ya aikata hakan ne saboda tsanar da yai wa yaron, inda ya ce shi ba zai iya ciyar da ɗan wani ba.
Ya ƙara da cewar, wanda ake zargin ya bayyana cewar, tun a baya ya taɓa yunƙurin kashe yaron, sai dai bai samu nasara ba, saboda mahaifiyar yaron ta gane nufinsa har ma ta kai ƙararsa wajen waliiyanta.
DSP Shiisu ya ce, tuni an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin ya fuskanci hukuncin laifin da ya aikata.