Wani mutum dan shekara 40 a duniya mai suna Arnold Masuka ya bukaci karamar kotu da ke Lusaka a kasar Zambia da ta warware auren da ke tsakaninsa da matarsa mai suna Hilda Mleya saboda tsananin kyan da take da shi.
Wani rahoto da jaridar ZAMBIA OBSERVER ta fitar ya bayyana cewa, Arnold ya bukaci kotu ta sakar masa matarsa ne saboda tsananin kyanta da yake hana shi bacci da daddare.
Bayanin Arnold na cewa yana rayuwa cikin tsananin tsoron rasa kyakkyawar matar tasa ga wani namijin ya tayar da hankalin mutane da kuma hukumomi musamman kuma da ya bayyana bukatar a sakar masa ita.
Ma’aikacin kotun da Arnolda ya shigar da kara, cikin tsananin mamaki ya bayyana cewa duk tsawon da shekarun da ya debe yana aiki a bangaren shari’a, bai taba ganin lamari irin wannan ba.
Shi dai Arnold ya kara jaddawa kotun cewa, tsoronsa na kar wani namijin ya kwace masa mata, shine ya sa shi yanke hukuncin cewa a sakar masa ita.