An rawaito cewa wani mutum ya fadi kuma ya mutu a dakin otel a Ada George da ke karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers bayan sakin labule da yarinyarsa a dakin.
Jaridar PUNCH ta gano cewa, al’amarin ya faru ne awanni kadan bayan mutumin da yarinyar tasa sun shiga otel din a awannin farko na ranar Laraba.
Wani da ke cikin otel din, wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, wajen karfe 2 na dare, yarinyar da suka shiga otel din tare da mutumin ta fice daga dakin ta shiga wani dakin domin ta sanar da cewa abokin zamanta ya fadi.
Mutumin ya baiyana cewa, manajan otel din da masu gadin otel din sun je dakin, inda suka gaggauta kai mutumin asibiti.
An gano cewa mutumin ya mutu a kan hanyar zuwa asibitin.
Haka kuma, wani wanda ya shaida abin da ya faru ya ce, matar ta ce, mamacin ya sha maganin kara karfin maza a wani waje dare daya kafin daren da ya mutu.
Lokacin da aka tuntubi mukaddashin mai magana da yawun ‘yansandan jihar, Grace Iringe-Kokom, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa an kama matar da kuma manajan otel din.
“Eh, rundunar ‘yansanda ta san da lamarin da ya faru a otel din, kuma ana cigaba da bincike a kai.
“Jami’anmu sun kama matar da kuma manajan otel din. Za kuma a sanar da abin da ya faru a gaba game da lamarin,” in ji Iringe-Kokom.
(PUNCH)