For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Mutum Ya Kashe ‘Ya’yansa 3 Ya Boye Gawarsu Firji

‘Yansanda a Enugu na bincikar wani dan shekara 52 mai suna Ifeanyi Amadikwa kan zargin kashe ‘ya’yansa uku masu suna Chidalum Amadikwa ‘yar shekara 11, Amarachi Amadikwa ‘yar shekara 8 da kuma Ebubechukwu Amadikwa dan shekara 4.

Amadikwa ya yi amfani da rashin matarsa a gida wajen kashe yaran su uku wadanda ya sanya gawarwakinsu a firji, kamar yanda Kakakin ‘Yansandan Jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe ya bayyana.

ASP Ndukwe ya ce, wanda ake zargin, Amadikwa, yana zaune ne a gida mai lamba 74 kan titin Nkwubor, da ke Emene kusa da Enugu, kuma an kama shi ranar 4 ga Janairu da misalin karfe 7:30 na dare.

Ya kara da cewa, mahaifiyar yaran ba ta nan, ta tafi kasuwa lokacin da Amadikwa ya aikata aika-aika.

“Binciken farko kan lamarin ya nuna cewa, matar wanda ake zargin kuma mahaifiyar yaran ta tafi kasuwa da danta namiji a ranar 4 ga Janairu inda ta bar sauran karkashin kulawar wanda ake zargin.

KU KARANTA: ‘Yan Bindiga A Plateau Da Niger Sun Kashe Mutane 52 Tare Da Kone Kauyuka

“Ta kuma dawo da yamma a wannan ranar inda ta samu yaran ba sa nan. Amma lokacin da tai kokarin binciken inda yaran suke sai wanda ake zargin ya nuna mata firjin da ya dawo da shi daga shagonsa ranar 2 ga Janairu ya kuma ajjiye shi a rumfar kofar dakinsu.

“Da aka duba sosai, sai aka sami gawarwakin yaran cikin firjin jikinsu duk da raunuka, wanda ya nuna an kashe su ne aka jefa su a ciki.”

ASP Ndukwe ya kuma ce, an garzaya da gawarwakin zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsu aka kuma ajjiye su mutuware domin yin bincike.

Ya kara da cewa, Kwamishinan ‘Yansandan jihar Enugu, Lawal Abubakar, ya yiwa mahaifiyar da sauran ‘yan uwa da abokan arziki jajjabi bisa mutuwar yaran.

Kakakin ‘yansandan, ya tabbatar da cewa, Kwamishinan ‘yansandan zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an binciki laifin tare da yin adalci.

Comments
Loading...