Wani mutum da aka bayyana sunansa da Mohammed Faworaja ya gamu da ajalinsa a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a lokacin da yake gujewa kare.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a kusa Asa Dam da ke yankin Warah-Osin a Ƙaramar Hukumar Ilorin ta Yamma da ke jihar.
Wata majiya da ta buƙaci a ɓoye sunanta ta ce, karen wanda kiwon Germany ne, ya kunce ne inda ya bi marigayin wanda ya buga ƙirjinsa a falwayar lantarki.
Marigayin ya mutu ne bisa zubar da jini da yake yi ta ciki a dalilin buguwar da ya samu.
Labari Mai Alaƙa: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ƴanmata Da Zawarawa 23 A Zamfara
An bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki mai haba-haba da mutane, wanda ke da shekaru kusan 33.
A lokacin jana’izar marigayin, mahaifinsa ya nuna matuƙar kaɗuwarsa, musamman kasancewar ya miƙa masa gudanar da iyalinsu saboda ritayar da yai ba da jimawa ba.
Da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’in ya tabbatar da cewa an kama mamallakin karen, sannan kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.
