Wani mutum mai suna Mr. Joel Udoh ya yi karar Ifeanyi na Cocin Loves Chapel a gaban kotun Majistare ta 39 a Kano saboda zarginsa da kwace masa mata.
Lauyan mai karar, Yusuf Ali Faragai ya ce, mai karar ya yi karar malaminsa na cocin Lovers Chapel da ke yankin Sabongari a Kano saboda zarginsa da kwace masa mata ta hanyar jan hankalinta.
Lokacin da aka gabatar da maganar a kotun, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin.
Mr. Joel daya ne daga cikin mabiya cocin Pastor Ifeanyi da ke unguwar Sabongari a Kano.
A bangarensa, Alkalin Kotun Majistare, Mustapha Hassan ya bayar da umarnin bincikar lamarin ga ‘yansandan da ke Zone One a Kano.
(NIGERIAN TRACKER)