Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya tabbatar da cafke wani mai siyar da ice cream mai suna Sani Musa dan shekara 35, da zargin yin lalata da yaro dan shekara 12.
Wakil ya ce, wanda ake zargin ya yaudari yaron ne zuwa wani rufaffen shago inda ya aikata mugun aikin.
Mai magana da yawun ‘yansandan ya ce, “A ranar 6 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 9 na safe, wasu masu bincike da ke ofishin ‘yansanda na Alkaleri, sun yi amfani da rahoton da suka samu, inda suka kama wani mai suna Sani Musa, dan shekara 35, mai siyar da ice cream da zargin yin lalata da yaro dan shekara 12. Lokacin da ake tuhumar mai laifin, ya amsa laifinsa.
A wani labarin kuma makamancin wannan, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Bauchin ya kara da cewa, rundunar ‘yansandan jihar ta kama wani mai bayar da maganin gargajiya, mai suna Monday Ishaku dan shekara 32, da laifin sanya wata mata maye da kuma yi mata fyade agidansa.
Wakil ya ce, “Mijin matar ya ce, ‘yarsa ‘yar shekara 19 ce bata da lafiya, kuma bayan an yi mata magani ba a samu nasara ba, sai ya yanke hukuncin kai ta ga Monday Ishaku wanda ya sanar masa cewa, matarsa ce ke jawowa ‘yar tasa jinyar.
“Sai ya dau alkawarin cewa zai musu magani gaba daya uwar da ‘yar da daddare. A lokacin hakan ne, wanda ake zargin ya yaudari masu neman lafiyar inda ya aikata mummunan aikin,” in ji shi.