For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Sarki A Yobe Ya Kai Ziyarar Haɗinkai Ga Sarkin Kano Sunusi

A ranar Lahadi, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya karɓi baƙuncin Sarkin Potiskum na Jihar Yobe, Umar Bauya, wanda shine na farko daga sarakunan Arewacin Najeriya da ya kawo masa ziyarar haɗin kai tun bayan da Gwamna Abba Yusuf ya mayar da shi matsayin Sarkin Kano.

Sarkin Potiskum, Umar Bauya, ya samu tarɓa daga sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a masarautar Kano a fadar Sarkin Kano.

A yayin ziyarar, Bauya ya bayyana goyon bayansa ga Sarki Sanusi, wanda kuma shine Shugaban ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya.

Bauya ya tuna wa Sanusi cewa tarihi ya maimaita kansa da dawowarsa a matsayin Sarki, yana mai cewa, “Haka ya faru da ni shekaru 26 da suka gabata kuma tare da taimakon Allah, na dawo cikin zaman lafiya da jama’ata.”

Ya ƙara da cewa dawowar Sarki Sanusi II alama ce ta jagoranci nagari, wanda yake yiwa al’ummarsa tunani da aiki mai kyau, don haka yana da cikakken goyon bayansa da na jama’arsa.

Bauya ya roƙi Sanusi da ya tallafa musu wajen kammala ginin Masallacin Juma’a a fadarsa, wanda suka fara shekaru uku da suka wuce amma aka dakata saboda matsalolin kuɗi.

Comments
Loading...