For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wani Sojan Gona Ya Damfari Mutane Tare Da Yaudarar Mata Yana Lalata Da Su

Jami’an ‘yan sanda na Rundunar ‘Yansanda ta jihar Akwa Ibom hadin guiwa da Sashin Binciken Manyan Laifuffuka a jihar, sun cafke wani da ake zargin dan damfara ne da ake kira da Mr. Imaobong Akpan yana yin sojan gona a matsayin Kwamishinan Kasa da Albarkatun Ruwa, Pastor Umo Eno.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Odiko MacDon, ya bayyana hakanne a bayan sun kama wanda ake zargin a ranar Talata.

Jami’an sun kama Mr. Imaobong tare da ajjiyeshi a ofishinsu da ke Ikot Akpan bisa korafin da suka karba kan lamarin.

Odiko ya bayyana irin kayayyakin da suka kama Mr. Imaobong da su, wadanda suka hada da layikan waya guda biyar, wayoyi biyu da kuma kudi dala bakwai da kuma yuan biyar.

Ya kuma tabbatar da cewa, wanda ake zargin bayan laifin yin sojan gonawa kwamishinan a Facebook ya kuma damfari wasu mutanen musamman ma mata wadanda yake baiwa aikin bogi bayan ya yi lalata da su.

KU KARANTA:

Odiko ya bayyana cewa “wanda ake zargin wanda kwararren dan damfara ne kuma mayaudarin mata, ya amsa laifinsa na kirkirar shafin Facebook na sojan gona.

“Yana amfani da wannan shafin wajen yaudarar ‘yan mata ya kai su otel ya yi lalata da su bayan ya yi musu alkawarin sama musu aiki, haka kuma ya damfari wadansu da dama miliyoyin kudade.

“Ya samu nasarar yaudarar mata goma ta hanyar shafin sojan gonarsa na Facebook inda yai lalata da su a matsayin mai temakawa kwamishina.”

Lokacin da wanda ake zargin ke bayani ga ‘yan jaridu, ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana cewa bai ma san tsautsayin da ya kai shi ga aikata aika-aikar ba.

Comments
Loading...