Daga: Haruna A Bultuwa
Kwanaki kadan bayan kashe wata yarinya Hanifa Abubakar mai shekaru biyar ‘yar jihar Kano da malamninta ya yi, an kuma kashe wata yarinya Asma’u bayan an yi garkuwa da ita da kuma karbar kudin fansa naira miliyan 3.45 a Zaria, jihar Kaduna.
Ana zargin makwabcinsu yarinyar Alhaji Shuaibu Wa’alamu ne ya sace Asma’u a ranar 9 ga watan Disamba, 2021.
Yarinyar mai shekaru takwas ta fita aike ne a ranar da aka sace ta, fitar da ba ta koma gida ba daga ita.
Mahaifin yarinyar ya bayyana cewa, “kwanaki kadan da sace yarinyar, masu garkuwa da ita suka fara kiran lambata, inda suka bukaci naira miliyan 15. Amma sai muka sasanta a kan na fara biyan naira miliyan 2.
KU KARANTA: Wanda Yai Garkuwa Da ‘Yar Shekara 5, Ya Kasheta Ya Daddatsa Gawarta
A cewar mahaifin Asma’u, “Sun karbi kudin ne a unguwar Rigasa da ke Kaduna. Daga baya, sai suka sake kirana suka bukaci a karin naira miliyan 1 da dubu 450 a matsayin sharadin sakin ‘yata.
Ya kara da cewa “Ban yi gardama ba na ba su kuɗin. Sai dai bayan an biya kudin fansa kamar yadda suka bukata, sai suka kira, suka sanar min cewa sun kashe ta, daganan suka rufe wayar su.
Mahaifin Asma’u ya bayyana cew “tunda farko yana bibiye da wadanda suka sace yar tasa, amma ina tsoron karsu kasheta, shi yasa nake yin duk abinda suka bukata.”
“Na san wadanda suka sace ta suka kashe ta. Suna kewaye da mu. Ina da hujja mai ƙarfi. Na fadawa ‘yan sanda. Hasali ma an kama wadanda ake zargin,” inji mahaifin Asma’u.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da rahotannin sace-sacen jama’a suka cika kafafen sada zumunta, ciki har da kisan Hanifa ‘yar shekara biyar, wadda malaminsu ya yi garkuwa da ita tare da kashe ta bayan ya bukaci a biyashi naira miliyan 6, kudin fansa.
(Vanguard)