For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasan Farko Na Cin Kofin Afirka Na Cike Da Rudani

A ranar Lahadi 9 ga watan Janairu ne Za’afara gasar cin kofin nahiyyar Afrika na 2021, wanda kasashe 24 zasu fafata.

Mai masaukin baki kasar Cameroon ce zata fara fafata wasan da misalin karfe 5 na yamma da abokiyar hamayyar ta Burkina Faso.

Yanzu haka dai akwai kimanin ƴan wasan Burkina Faso 7 da aka tabbatar da cewa sun kamu da Cutar Corona bayan gwajin da akayi musu kasa da awanni 24 kafin a fara wannan gasar, amma mahukuntan tawagar Kungiyyar kwallon kafa ta Burkina Faso tayi watsi da sakamakon gwajin inda tace ” an shirya sakamakon ne domin a rage karfin Kungiyyar don Cameroon ta samu nasara.

Burkina Faso ta bukaci a sake yiwa ƴan wasan na ta gwajin domin tabbatar da sahihancin gwajin farko.
Kasar Cameroon,Burkina Faso, Ethiopia da Cape Varde suna a rukunin A ne kuma zasu fafata a tsakanin su.

Ga jerin kasashen da zasu fafata da inkiyar su.
🇨🇲 Cameroon – Indomitable Lions
🇧🇫 Burkina Faso – The Stallions
🇨🇻 Cape Verde – Blue Sharks
🇪🇹 Ethiopia – Walia Ibex
🇸🇳 Senegal – Teranga Lions
🇿🇼 Zimbabwe – The Warriors
🇬🇳 Guinea – Syli Nationale (National Elephants)
🇲🇼 Malawi – The Flames
🇲🇦 Morocco – The Atlas Lions
🇬🇭 Ghana – The Black Stars
🇬🇦 Gabon – The Panthers
🇰🇲 Comoros – The Coelacanths
🇪🇬 Egypt – The Pharaohs
🇳🇬 Nigeria – Super Eagles
🇸🇩 Sudan – Falcons of Jediane
🇬🇼 Guinea-Bissau – Djurtus
🇩🇿 Algeria – The Fennec Foxes
🇨🇮 Ivory Coast – The Elephants
🇸🇱 Sierra Leone – Leone Stars
🇬🇶 Equatorial Guinea – Nzalang Nacional (National Thunder)
🇹🇳 Tunisia – Carthage Eagles
🇲🇱 Mali – Les Aigles (The Eagles)
🇬🇲 Gambia – The Scorpions
🇲🇷 Mauritania – Lions of Chinguetti

Daga: Muhamamad Suleiman Yobe

Comments
Loading...