For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasiƙa Ga Gwamnan Jigawa, Umar Namadi Kan Gyaran Ilimi

Daga: Haruna Shu’aibu Ɗanzomo

Maigirma Gwamna, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin.

Tabbas hankali yana kan abubuwa guda uku a Jihar Jigawa wanda tsawon mulkinku na shekaru 8 wato daga 2015 zuwa 2023 sam ba ku basu kulawa ba, kuma an samu koma baya a cikin lamuran – abubuwan kuwa sune ILMI, LAFIYA, da kuma NOMA.

Waɗannan abubawan sune ginshiƙan Jihar Jigawa, amma duk kun lalata su a shekarunku takwas na farko. A yanzu ma kuma akwai alamun baka shirya kawo gyara ba musamman ma a fannin Ilimi.

Kawo yanxu duk wasu turakuna da zasu jagoranci harkar ilimin Jihar Jigawa ka gama kafa su, ammafa ga alama ka kalli alaƙarka da su ko kuma tarin shedar karatunsu (ccertificates) ka ba su muƙamai, amma ba ka kalli abin da  fannin ilimin yake buƙata ba.

Da Kwamishinan Ilimi na Manyan Makarantu hadi da Kimiyya da Fasaha da kuma Shugaban SUBEB, a maganar gaskiya akwai kuskure a ciki, domin ba farfesanci kawai muke buƙata ba. Muna buƙatar mutanen da suka san Jihar Jigawa da halin da ilimin Jihar Jigawa yake ciki domin tunkarar gyaransa.

Na tabbatar idan ka tambayi waɗannan farfesoshin adadin makarantun primary da secondary da suke Jihar Jigawa sai dai su faɗa maka abin da suka gani a Goggle, hakama idan ka tamabaye su yawan ɗalibai da yawan malamai da kuma adadin malaman da ake buƙata domin a cike gurbi basu sani ba. Hakama idan ka tambaye su halin da makarantun suke cike, abin da ya shafi gine-gine da kayan aiki, duk ba su sani ba.

Shekarun 2007 zuwa 2015, lokacin da Sule Lamido yake Gwamnan Jihar Jigawa ya yi amfani da Farfesoshi a matsayin kwamanshinonin ilimi amma kuma sauran muƙarabban nasu duk ƴan Jihar Jigawa ne, kuma duk mazaunan Jihar Jigawa ne, kuma duk ma’aikatan Ma’aikatar Ilimi ne, sannan sai da ya duba mutane masu ƙwazo da kuma tsananin tsayuwa a kan aikinsu, kamar Mallam Sani A’I da kuma irin su Nagodi, duk Jihar Jigawa sai da ta san an zo da sabon tsari akan ILIMI.

Hikimar ita ce idan kwamanshina kuma Farfesa ya san yadda ake magance matsalar ILIMI a rubuce su kuma waɗannan sun san ilimin a zahiri kuma sun san Jihar Jigawa a zahiri kuma sun san matsatstsalun a zahiri kuma sun yadda za a magance su a zahiri.

Amma fa waɗannan da ka haɗa wallahi ba na jin sun san me ya kamata su yi ma, don haka suna buƙatar lokaci mai tsawo aƙalla su fahimci abokan aikinsu da aikinsu da kuma inda zasu yi aikin.

Maigirma gwamna ka sake dubawa kuma ka yi nazari sosai ka da ka yadda da masu ce maka komai ka yi daidai ne, idan ka gama sune zasu fara zame maka baya.

Ina fatan gyara kayanka ba zai zama sauƙe mu raba ba.

Daga: Haruna Shu’aibu Danzomo

Comments
Loading...