For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasu Ƴan Ƙasashen Waje Ne Ke Shigo Mana Da Matsalar Tsaro – Buhari

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari a ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayyana cewa ba za a aminta da yawan hare-haren da ke faruwa a ƙasar ba, inda ya zargi wasu ƴan ƙasashen waje da iza wutar matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

Da yake jawabi a Abuja, a wajen bikin yaye ɗalibai ƴan kwas na 30 na makarantar National Defence College inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya wakilce shi, Shugaban Ƙasar ya ce, “Gwamnati ta matuƙar damuwa da ayyukan ƴanbindiga da ɓatagari waɗanda suke renon munanan ƴaƴansu a wasu sassa na ƙasar. Wannan ya samo asali ne ganin yanda hare-hare a kan ƴan ƙasa ke ta ƙara ƙaruwa. Wannan abu ne da ba za a yarda da shi ba.

“A kan haka, mun baiwa sojoji ƙaƙƙarfan umarni da sauran jami’an tsaro da kar su saurarawa ƴan ta’adda, ƴan bindiga da sauran maƙiya ƙasa. Haka kuma, mun samar da haɗin guiwa domin magance matsalar tsaron kan iyaka da na cikin teku saboda mun gano cewa, wasu daga matsalolin tsaronmu ƴan ƙasashen waje ne ke shigo mana da su.

“Ina so na tabbatarwa ƴan Najeriya cewa, gwamnati na yin iya bakin ƙoƙarinta domin magance ko kame ɓatagarin ko ƴan bindigar a ko’ina suke.”

Comments
Loading...