Al’ummu guda uku da ke ƙaramar hukumar Ojo a Jihar Lagos, sun ƙalubalanci kuɗin wutar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Eko Electricity Distribution Company,
EKEDC, ke kintata musu su biya.
Al’ummun sun je babban ofishin kamfanin ne da Marina domin nuna fushin nasu.
Sun buƙaci kamfanin da ya magance matsalar ta hanyar samar musu da mitocin da zasu na saka kuɗi suna shan wutar maimakon a kintata musu abin da zasu biya.
Al’ummun sun haɗa da Agric, Onireke, da Owode, waɗanda suka sami wakilcin Ƙungiyar Ci Gaban yankinsu da kuma wasu mutanen.
Rukunin wakilan da suka je ofishin kamfanin sun haɗa da, shugabannin matasa, mazauna unguwannin da mata ƴan kasuwa daga yankin.
Shugaban Al’ummar Agric, Mr. Abiodun Bamgboye ne ya jagoranci mutanen, inda ya ce, sun je ofishin ne bayan an gaza magance ƙorafe-ƙorafen da aka sha kaiwa kamfanin na cajin kuɗi mai yawa alhali wutar ba ta samuwa kamar kuɗin da ake caja.
Ya buƙaci kamfanin da ya yi bincike kan lamarin, sannan ya tsayar da ƙaruwar kuɗaɗen da ake samu a kan bill ɗin da ake rarraba musu duk wata.
“Bamu san me yasa suke ta ƙara kuɗin bill ɗinmu ba; yanzu haka kuɗin lantarki yana kaiwa kuɗin hayar gida,” in ji wani shugaban matasa da ke wakiltar Onireke, Mr. Jamiu Adeosun.
Ɗaya daga cikin ma’aikatan kamfanin EKEDC wanda ya karbi mutanen, ya gaiyaci shugabannin al’ummun guda uku domin ganawar sirri.