
Bankunan ajjiye kudade a Najeriya sun fara yin biyayya ga umarnin Kotun Koli na amincewa da tsoffin naira 1000 da 500 da 200 a matsayin kudaden mu’amala har nan da watanni 10 goma masu zuwa.
Kotun Kolin dai a karshen makon jiya, ta bayar da umarnin cewa, tsoffin kudaden naira su dawo su ci gaba da zagayawa a tsakanin al’umma tare da sabbin kudade har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Kotun ta ce, yunkurin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin kudi ya sabawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
WANI LABARIN: Gobara Ta Lakume Dukiya Mai Yawa A Kauyukan Jigawa
A ranar Litinin ta jiya, bincike ya nuna cewa, bankuna sun fara yin biyayya ga umarnin Kotun Kolin, duk da kasancewar har kawo yanzu bangaren Gwamnatin Tarayya da kuma Babban Bankin Najeriya ba su ce komai ba game da umarnin.
Binciken da wakilan Jaridar PUNCH da DAILY TRUST suka yi, ya nuna cewa wasu bankuna a biranen Lagos, Kano, Abuja da wasu manyan biranen kasar sun fara bayar da tsoffin kudaden ga kostomominsu a jiya Litinin.
Sai dai kuma, sauran bankuna da dama sun ki baiwa kostomomi tsoffin kudaden, yayin da suke bayyana cewa, ba zasu yi hakan ba har sai sun sami umarni daga Babban Bankin Najeriya, CBN.