Gungun mata ‘yan siyasa karkashin Kungiyar Mata a Siyasa, sun yi barazanar gurfanar da jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP kan zargin da suke na nuna wariya ga mata a Babban Zaben jam’iyyar da ke karatowa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, gungun matan na zargin cewa, jam’iyyar na shirin cire mata daga masu gudanar da Babban Taron jam’iyyar da za a gudanar a ranakun 30 da 31 ga watan October, 2021 ta hanyar samar da tsarin sasanton da zai fifita maza a samun mukaman jagorantar jam’iyyar.
Matan sun bayyana cewa, wannan na faruwa ne duk da tanadin da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na mika kaso 35% na mukaman jam’iyyar ga mata.
Shugabar Kungiyar Mata a Siyasa, Ebere Ifandu ce ta fitar da gargadin a wani taron ganawa da ‘yan jaridu a Abuja ranar Laraba.
Shugabar ta ce, abin takaici ne cewa, duk da tanadin da ke kunshe a kundin tsarin mulkin jam’iyyar shugabancin maza ya kanainaye mukaman jam’iyyar ta hanyar samar da sasanto.
Ta bayyana goyon bayan kungiyarta ga tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Inna Ciroma a kudirinta na neman mukamin mataimakiyar shugabar jam’iyyar ta kasa a yankin Arewa.
Ebere ta ce a kokarin kungiyar na nuna wannan goyon baya, ‘yan kungiyar ne suka siyawa ‘yar takarar takardar neman takarar.
Ta kuma roki Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa ta sanya tanadin doka da zai kare hakkokin mata a kokarin da ake na gyaran dokokin zabe.