Mutanen da ba su gaza 11 ba ne aka tabbatar sun mutu a ƙauyukan Igama da Edumoga Ehaje da ke Ƙaramar Hukumar Okpokwu ta Jihar Benue.
Ana zargin makiyaya da kai harin wanda ya faru a jiya Lahadi.
An sanar da jaridar THE NATION cewa, maharan sun kuma ƙone gidaje da dama a garuruwan.
Harin dai ya sanya fargaba a zukatan makwabtan ƙauyuka, waɗanda aka ce sun ƙauracewa gidajensu, bayan faruwar lamarin a jiya.
Sanata Abba Moro ya tabbatar da faruwar lamarin kan ƙauyukan biyu a wani rubutu da yai a dandalin Facebook.
Sanatan dai shi ma ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Okpokwu ne, inda ƙauyukan da aka kai wa harin suke.
Mai magana da yawun ƴansanda a Jihar Benue, Kate Anene ba ta daga kiran da akai mata ba, haka kuma, ba ta amsa sakon kar-ta-kwanan da wakilin THE NATION ya tura mata ba.