Wasu manyan ƴan siyasa da suka fusata a Jihar Jigawa, sun yi wani abu mai kama da gangamin juyawa Gwamna Muhammad Badaru Abubakar baya har da ɗaukar matakin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP.
Waɗanda suke kan gaba-gaba a wannan yunƙuri sun haɗa da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Ahmed Mahmud Gumel, Sanata Sabo Muhammad Nakudu, tsohon ɗan Majalissar Wakilai, Bashir Adamu Jumbo.
Sauran sun haɗa da tsohon ɗan Majalissar Wakilai, Gausu Boyi Ringim, ɗan Majalissar Jiha, Musa Sule Dutse, tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutse, Bala Ƴargaba da sauran su.
An gano sanannun ƴan jam’iyyun APC da PDPn ne a wasu hotuna tare da jagoran jam’iyyar NNPP na Jihar Jigawa, Malam Aminu Ibrahim Ringim, wanda aka ɗauka bayan kammala wani muhimmin zama.
Jagoran Jam’iyyar NNPPn ne ya sauƙi baƙin a gidansa da ke Kano.
Wasu daga cikin waɗanda suka marawa Malam Aminu Ibrahim Ringim baya a zaman, sun haɗa da Maisudan, Garba Ilyasu Yalwan Damai, Safiyanu Taura, Aminu Infor Babura, Murtala Arrow, Musa Kazaure, Lawan Kazaure, da sauran ƴan jam’iyyar NNPP na jihar Jigawa.
Da yake magana kan gaskiyar batun, wani jagora a NNPP, Lawan Kazaure, ya tabbatar da cewa wasu manya daga jam’iyyar APC da PDP sun nuna sha’awarsu ta shiga jam’iyyarsu.
Ya ƙara da cewa, an yi zaman ne a matsayin shirye-shirye na karɓarsu a cikin jamiyyar, inda ya kuma ce akwai wasu ma da dama da zasu shiga jam’iyyar ta NNPP a Jigawa nan ba da jimawa ba.
Da yake musanta batun, Olu Katanga, ɗaya daga cikin magoya bayan Bashir Adamu Jumbo, ya yi watsi da jita-jitar cewa ubangidan nasa ya koma jam’iyyar NNPP, inda ya ce har yanzu Jumbo ɗan jam’iyyar PDP ne.
Shima Bilyaminu Ibrahim Excellency ya bi bayan Olu Katanga, inda ya ce Bashir Adamu Jumbo bai nuna sha’awar shiga jam’iyyar NNPP ba.
Rahotanni dai sun nuna cewa, mafi yawan waɗanda suka halarci zaman, wasu mutane ne da suka faɗi zaɓe ne a zaɓuɓɓukan fitar da gwanaye da akai a jam’iyyun da suke shirin bari.