For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasu Maza 4 ‘Yan Anambra Sun Hadu Sun Yiwa Wata Yarinya Fyade Saboda Laifin Babanta

Hukumar Hana Safarar Mutane reshen Jihar Anambra, hadi da ‘yan kungiyar sintiri ta vigilante, sun kama wasu mutane uku saboda yiwa wata yarinya ‘yar shekara 13.

Jaridar PUNCH ta gano cewa, akwai wadanda ake zargi guda hudu a lamarin, sai dai kuma uku daga ciki ne aka kama, na hudun ya tsere lokacin da jami’an tsaro suka kai mamaye yankin Nkapor, kusa da Onitsha a Jihar Anambra.

Kwamishiniyar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a ta jihar, Ify Obinabo ce ta bayyana faruwar lamarin ga ‘yanjarida a garin Awka a jiya Laraba ta hannun mai taimaka mata a bangaren yada labarai, Chidimma Ikeanyionwu.

Ta ce, tuni an mika wadanda ake zargin ga shelkwatar ‘yansanda da ke Awka inda za a yanke musu hukunci, yayin da ta tabbatarwa wadda aka ci zarafin cewa za a kwato mata hakkinta.

A lokacin da ake tuhumar masu laifin, biyu daga cikinsu sun amsa laifinsu yayin da suka nemi afuwa, bayan sun bayyana cewa sun aikata laifin ne saboda sabanin da suka samu da baban yarinyar.

Shi kuma wanda ake zargi na ukun, ya bayyana cewa, shi ya je gurin ne kawai lokacin da ake aikata laifin amma babu shi a ciki; sai dai kuma daya daga cikin sauran biyun ya ce, shi wanda ya ki amincewar shine ma na biyu a wajen yiwa yarinyar fyaden.

Wadda aka yiwa aika-aikar ta ce, masu laifin abokan zamansu ne a gida daya, amma sai suka dauke ta suka kai ta Kogin Nkisi domin su yi mata fyade bayan sun sami sabani da mahaifinta.

Comments
Loading...