For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasu Mutane Sun Kashe Mai Kashe Yara A Yammacin Kenya

Wani gungun mutane a Yammacin kasar Kenya ya kashe wani mutum mai kisan mutane da ya amsa laifinsa, wanda ya tsere daga hannun ‘yan sanda kwana uku da suka gabata, a cewar hukumar ‘yan sandan.

Gungun mutanen sun gano Masten Wanjala mai shekaru 20 a wani gida a garin Bungoma kuma suka yi ta dukansa har ya mutu, a cewarsu.

Hukumomi sun kaddamar da wani gagarumin bincike don gano mai laifin wanda ya amsa laifin kashe yara maza kanana fiye da 10 cikin shekaru biyar.

Ya kuma amsa laifin cewa yana ba su miyagun kwayoyi kuma a wasu lokutan ma yana shan jininsu.

Rahotanni da BBC ta tantance sun nuna cewa ya koma gidan iyayensa wadanda suka tsine masa, kuma daga karshe makwabta suka shake shi bayan sun gano yana gidan iyayen nasa, kamar yadda wani shaida ya bayyana wa jaridar Standard ta Kenya.

Ana tunanin cewa iyayensa ne suka gano gawarsa, yayin da ‘yan sanda suka ce suna ci gaba da bincike kan lamari.

Comments
Loading...