For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasu Mutane Sun Yanka Wata Mai Zaman Kanta A Jigawa

Rundunar ‘Yansanda a Jigawa sun tabbatar da kisan wata mata ‘yar shekara 35 da haihuwa mai suna Ladi Anndu bayan wasu mutane da ba a san suwaye ba sun farmaketa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 8:45 na dare a Unguwar Gandu da ke garin Hadejia.

Mai magana da yawun ‘yansanda a jihar Jigawa, Lawan Shiisu ne ya baiyanawa manema labarai faruwar lamarin.

Lawan Shiisu ya ce wata da ake kira da Linder Geoffrey kuma ‘yar uwa ga wadda aka kashe din ce ta baiyanawa ‘yansandan faruwar lamarin.

Linder ta ce, wasu mutane ne suka kutsa dakin Ladi Anndu inda suka yanka ta da abu mai kaifi.

Mutanen dai sun yiwa Ladi yankan rago ne abin da ya sa aka garzaya da ita asibiti domin ceton lafiyar ta amma daga bisani ta mutu.

Lawan Shiisu ya ce an samu almakashi cikin jini a wajen da abun ya faru a matsayin shaida.

Ya kuma ce ‘yansanda sun kai samame yankin da nufin kama masu laifin.

(NAN)

Comments
Loading...