For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wasu Sanatocin Sun Samu Naira Miliyan Biyu Ta Shiga Hutunsu – Sanata Ningi

Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Mazaɓar Sanata ta Bauchi ta Tsakiya ya ce, wasu ƴan majalissar sun samu naira miliyan biyu a matsayin kuɗin alawus na hutunsu, duk da dai shi bai samu nasa ba.

A wani yanayi da sanatocin ba su so ba, Shugaban Sanatocin, Godswill Akpabio ya faɗawa sanatocin cewa su tsammaci wani ɗan abun hasafi domin su ji daɗin yin hutunsu.

Ƴan kwanaki bayan alƙawarin na Akpabio wanda ya jawo cecekuce a tsakanin ƴan Najeriya, Sanata Ningi na Jam’iyyar PDP ya tabbatar da cewa, wasu sanatocin sun samu alawus ɗin nasu kamar yanda Akpabio yai alƙawari.

Sai dai kuma, Sanata Ningi ya ce shi har jiya shi babu abun da ya shiga masa cikin asusunsa, sai dai yana fatan ya samu bayan sun gama gyara abubuwan.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Ƙirƙiri Kwamiti Na Musamman Kan Zaɓen Jihohin Bayelsa, Imo Da Kogi

Sanatan na wannan magana ne a jiya Juma’a ta cikin shirin siyasa na Politics Today na gidan talabijin na CHANNELS.

Sanata Ningi ya bayyana abun da Akpabio yai a matsayin wanda bai kamata ba, inda ya ce ba haka ya kamata shugaban nasu ya tafiyar da lamarin ba.

Ya ce abun da ya farun zubewar kima ne ga Shugaban Majalissar da kuma Majalissar Sanatocin, inda ya ƙara da cewa, kamata yai shugaban ya bayyana ƙarara waɗanne kuɗaɗe ne za a tura da kuma abun da za ai da su.

Sanata Abdul Ningi ya ce shima bai ji daɗin lamarin ba kamar dai sauran ƴan Najeriya, sannan kuma ya ce yana ta tunanin ko kuɗin na mene ne shima.

Ya ƙara da cewa, idan sanatocin suka dawo daga hutun da suke, zasu buƙaci su ji ko kuɗin na mene ne, tun da dai a ƙa’ida ba a ba su alawus na tafiya hutu.

Comments
Loading...