Wasu daga cikin wadanda aka kafa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Jigawa da su karkashin Kungiyar Masu Ruwa da Tsaki ta jam’iyyar APC, sun mika korafinsu ga Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar, Mai Mala Buni, inda sukai zargin Gwamna Badaru da danne musu hakkokinsu na ‘yan jam’iyya.
‘Yan APC a Jigawa, sun kuma bukaci gaggauta soke zaben shugabannin jam’iyyar da aka gabatar a jihar.
A watan ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne dai masu ruwa da tsakin suka mika korafin nasu, yayin da suka tura tuni kan korafin ga kwamitin rikon jam’iyyar na Mai Mala Buni a ranar 23 ga Disamba na shekarar 2021.
Mutane shida ne suka sanyawa korafin hannu, wadanda suka hada da Alhaji Sani Ibrahim Taura, Barrister Hafizu Abubakar, Alhaji Bala Idi Kazaure, Mutari Garba Garki da Saifullahi Muhammad Mudassir.
Sun bayyana cewa, Gwamna Badaru, shi kadai ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar wanda aka karshe aka ce Alhaji Aminu Sani Gumel ne shugaban APC a Jigawa tare da sauran wadansu su 35 a matsayin sauran shugabanni.
“La’akari da korafin da muka rubuto mai kwanan wata 30 ga watan Oktoba, 2021 muka bayar a ofishinka, a matsayinmu na masu ruwa da tsaki wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina jam’iyyar APC a Jigawa, mun rubuto wannan ne domin mu yiwa ofishinka tuni cewa, akwai bukatar aiwatar da adalci kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar.
“Shugabancin jam’iyyar APC a Jigawa, yana cikin halin ha’ula’i a hannun Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, wanda shi shi kadai ya gudanar da zaben shugabanni inda aka samar da Alhaji Aminu Sani Gumel a matsayin shugaban jam’iyyar tare da wasu su 35.”
Masu ruwa da tsakin a jam’iyyar APC reshen Jigawa, sun rubuta a korafin nasu cewa, abin da yakamata da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulkin APC sun sha wuya a ranar 16 ga watan Oktoba na 2021 da sunan zaben shugabannin jam’iyyar a jihar Jigawa.
“Mu wadanda suka sa hannu a wannan takarda, kuma masu dauke da katin jam’iyyar APC, a matsayinmu na masu kishin jam’iyyar a jihar Jigawa, mun lura da yanda akai wancakali da hanyar da ta kamata, da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu a ranar 16 ga watan Oktoba, 2021 da sunan zaben shugabannin jam’iyya reshen jihar Jigawa.
“Ba mu ji dadin yanda aka gudanar da abin da aka kira da zaben shugabannin jam’iyya ba, wanda ya samar da Alhaji Aminu Sani Gumel tare da wasu su 35 a matsayin shugabannin jam’iyyar a jihar saboda dalilai kamar haka:
“Babu wani ingantaccen sasanto da akai wanda ya samar da shugabancin yanzu, saboda ba duk masu ruwa da tsaki aka tuntuba ba, babu takardar takara da ka fitar domin siyarwa ga sauran ‘yan jam’iyya in banda wadanda aka zaba don Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
“Babu wani daidaito da aka samu tsakanin ‘yan jam’iyya wadanda suka gina jam’iyyar a jihar wajen raba mukaman shugabancin. Musamman ma, masu ra’ayi a jam’iyyar daga bangaren ANPP, CPC, da AC ba a kula da su ba, Gwamna shi kadai ya zabi shugabannin ya kuma nada su kan jagorancin jam’iyyar duk da kasancewarsu wadanda ‘yan jam’iyya na asali ba su ma san su ba.