Wasu ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin Najeriya sun gurfanar da kwamatin shugabancin jam’iyyar na riko karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a gaban Babbar Kotun Abuja.
Mutanen su su biyar da suka hada da Suleiman Usman da Muhammed Shehu da Samaila Isahaka da Idris Isah da Audu Emmanuel, na neman kotun ta dakatar da gwamnan da kwamatinsa gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a watan Fabarairu mai zuwa, kamar yadda kafar Channels TV ta ruwaito.
Cikin karar da suka shigar mai kwanan watan 4 ga Janairun 2022, sun gurfanar da jam’iyyar APC da shugbanta da kuma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.
KU KARANTA: Gazawar APC Na Magance Rigingimun Ta A 2021 Kan Iya Yi Mata Sartse A Zaben 2023
Lauyan masu shigar da karar, Olusola Ojo, ya bayyana cewa suna bukatar a dakatar da taron ne saboda, a cewarsu, har yanzu wasu daga cikin tarukan a matakin jihohi ba su kammala ba.
Sun nemi kotun ta amsa tambayoyi biyar sannan ta ba da umarni guda takwas.
Idan har taron jam’iyyar APC ya tabbata, a yayin taron ne za a zabi shugabanta na kasa kamar yadda aka yi a matakin jihohi da mazabu, abin da har yanzu wasu ke takaddama a kai.
Daga: BBC Hausa