Wasu ‘yan-bindiga da ba a tantance ba, sun kashe Sule Mathew, dalibin da ya kammala karatun digiri na farko da shaidar 1st Class a sashin koyon ilimin sadarwa na Jami’ar Bayero da Kano, BUK.
‘Yan-bindigar sun kashe Sule Mathew ne a kan hanyarsa ta zuwa Anambara tare da sauran fasinjoji.
Mathew ya karanci Information and Media Studies kuma ya kammala da 1st Class a Tsangayar Koyon Ilimin Sadarwa ta BUK, sannan kuma ya nemi kwarewar aiki a PRNigeria.
An kashe shi da sauran fasonjojin cikin motarsu, a garin Ekwulobia, daya daga cikin manyan biranen Anambara bayan Awka, Onitsha da Nnewi.
An baiyana cewa, gawarwakin wadanda aka kashe din suna asibitin General Hospital Ekwulobia.
Wani abokin karatun Mathew wanda kuma suka yi koyon aiki a PRNigeria tare, Salis Manager, ya baiyana cewa, Mathew zai fara shirin bautar kasa, NYSC a cikin wadanda za su fara sati mai zuwa kafin a kashe shi.
Mathew ya yi aiki da PRNigeria a matsayin mai koyon aiki a shekarar 2019 a ofishinsu na Kano, sannan mahaifinsa ya rasu a watan Yunin da ya gabata lokaci kadan kafin fara rubuta jarabawarsa ta karshe a BUK, sannan kuma ya samu nasarar kammalawa da 1st Class.
(PRNigeria)