Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya a Najeriya ta shawarci Sarki Sunusi Lamido Sunusi da ya girmama umarnin Babbar Kotun Tarayya, ya sauƙa daga karagar mulkin Kano nan take.
Sarakunan sun ce, hukuncin kotun da ta bayar ranar Talata, hukunci ne na ƙarshe, kuma an samar da shi ne domin a samar da zaman lafiya a Jihar Kano.
A sanarwar da ta samu sanya hannun Shugaban Ƙungiyar, Cif Ameh Adaji, da Sakataren Ƙungiyar, Cif Danladi Etsu, ƙungiyar ta bayyana cewar, bai kamata sarki yai jagoranci ba tare da samun goyon bayan al’ummarsa ba, haka kuma ƙaƙaba kai a gadon sarauta, wani abu ne da ba a yarda da shi ba a duk faɗin duniya.
Sarakunan sun ce, matakin ƙarshe da za a ɗauka kan Sarki Sunusi shine na tilastashi ya bar gadon sarautar Kano, inda kuma su kai kira ga Sarkin da ya gujewa faruwar hakan a kansa don gudun faɗawa cikin wulaƙanta da tayar da hatsaniya a al’umma.