For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wata Kungiya A Hadejia Ta Shirya Taron Wayar Da Kan Masu Amfani Da Kafafen Sada Zumunta

Kungiyar sa kai ta matasa masu kishin kasar Hadejia mai suna Hadejia Youth Volunteers Association, HAYVA ta shirya taron wayar dakan matasa masu amfani da kafafen sada zumunta na zamani a dakin taro na UBJ Mall dake cikin garin Hadejia.

Taron wanda aka fara shi da yammacin ranar Litinin ya samu halartar masana, malamai, masu sarauta da matasa wanda aka gabatar da jawabai masu ratsa jiki kan amfanin kafafen sadarwa na zamani.

Malami A Kwalejin Ilimi dake Gumel, Aji Kima Hadejia shine ya bayyana makasudin wannan taro da kuma lokacin da aka dauka ana tanadin wannan ranar.

Da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Kuma Mamallakin Kamfanin UBJ, Alhaji Umar Babuga Jibir, ya bayyana cewa sun kirkiri wannan taro ne don seta kalamai da rubutun matasan yankin musamman yadda suke amfani dasu a wannan zamani.

Babuga ya kara da cewa kamata yai matasa su yi amfani da kafafen sada zumunta don samarwa da yankin cigaba ba wai batun kare wasu ba.

Alhaji Babuga ya nuna farin cikinsa kan yadda matasan suka nuna gamsuwarsu da jin dadinsu da wannan taron karfafawa da wayar da kan.

Shima anasa Jawabi Wakilin Mai Martaba Sarkin Hadejia, Muhammad Makama Shehu, Dan Madamin Hadejia, ya nuna farin cikinsa da gamsuwarsa kan wannan taron domin samar da cigaba ga masarautar baki daya.

A karshe matasa sun  bayyana jin dadinsu da gamsuwar su kan wannan taro da kuma fatan yin aiki da abubuwan da aka sanar musu a taron.

Wannan ne de karo na uku da kungiyar sa kai ta HAYVA ta shirya irin wannan taro.

Daga: Abubakar M Taheer Hadejia

Comments
Loading...