‘Yansanda a Jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudun Najeriya sun dakatar da yunkurin safarar yara tare da kubutar da yarinya ‘yar shekara 5 wadda aka siyarwa wani a Jihar Imo kan kudi naira 600,000.
An dai sace yarinyar ne a kauyen Omagwa da ke Karamar Hukumar Ikwerre ta Jihar Rivers bayan yarinya ta bata a ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 2022.
Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar, Friday Eboka ne ya bayyana hakan a ofishin ‘yansandan jihar da ke Port Harcourt, ranar Laraba, lokacin da yake duba mutane 30 da aka tsare saboda zarginsu manyan laifuffuka daban-daban.
Eboka ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.
Kwamishinan ya ce, a ranar 20 ga watan Mayu, wata mata mai suna Peace Emmanuel ta sanar da batan ‘yarta mai shekaru biyar a duniya a ofishin ‘yansanda na Omagwa.
Daga bisani ne kuma ofishin ya mika batun zuwa babban ofishin ‘yansanda na jihar da ke Port Harcourt wajen ‘yansanda na musamman masu bincike.
Jami’an ‘yansandan sun fara bincike nan take, inda suka gano cewar, kanwar babar yarinyar ce ta kitsa sace yarinyar, inda kuma ta siyar da yarinyar ga wata mata a Jihar Imo kan kudi naira 600,000.
Kwamishinan ya kara da cewa, jami’an sun kubutar da yarinyar tare da kama wadanda ake zargi su su biyu.
Babban wanda ake zargi a laifin wata ce mai suna Ejike Edith ‘yar shekara 30, inda ta bayyana sunayen wasu karin mutum biyu wadanda suka yi laifin tare.
Mutane biyun sune, Prince Ugwu da Nkiruja Samuel dan shekara 26.
Su ma sauran mutane biyun jami’an ‘yansandan sun samu nasarar cafke su, sai dai kuma mutumin da ya karbi yarinyar yana Jihar Imo, yayin da kwamishinan ya ce, suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kama shi domin ya fuskanci hukunci.