For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Wata Uwa Ta Yasar Da Jaririnta, Ta Bar Wasika A Tare Da Shi

An gano wani jariri sabuwar haihuwa tare da rubutacciyar wasikar da mahaifiyarsa ta bari a tare da shi a yankin Arewa maso Yammacin Cameroon.

An tsinci yaron ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu, 2023 a gefen MIDENO da ke unguwar Ntefinki a Nkwen, Bamenda, an kuma tsince shi cikin koshin lafiya, sannan an mika shi zuwa wajen ci gaba da kula da lafiyarsa.

A wasikar da mahaifiyar jaririn ta bari ta bayyana cewa, ba ta da wani zabi ban da ta yi abin da ta yi, saboda ba ta da wadatar iya kulawa da yaron, sannan ba ta da kowa.

Ta bukaci da a temaka a kula da jaririn, sannan kuma ta rubuta cewa ta sanya masa suna Migael tare da rubuta bayanan ranar haihuwarsa da kuma bayanin allurar rigakafin da aka yi masa.

An haifi Migael ne ranar 26 ga watan April, 2023 sannan kuma an masa allurar rigakafi ta BCG.

Wata kungiya da ke kula da irin wadannan matsaloli tana kan bincike kan samarwa jaririn kyakkyawar makoma.

Ga hoton wasikar da mahaifiyar jaririn ta bari:

Comments
Loading...