Wata uwa ‘yar kasar India ta yi fada da damisa da hannayenta domin ta tserar da karamin yaronta mai rarrafe daga bakin damisar.
Rahoto daga hukumomi a kasar a yau Labara ya nuna cewa, matar mai suna Archana Choudhary ta fito daga gidanta ne da ke tsakiyar jihar Madhya Pradesh a ranar Lahadi da daddare lokacin da ta fahimci danta mai watanni 15 a duniya na bukatar biyan bukata.
Wata damisa da ake da tabbacin cewa ta fito ne daga wajen killace damisu na Bandhavgarh ta tasowa uwar da yaron.
Ta kai harin kuma ta yi kokarin gatsa kan yaron da fikokinta amma mahaifiyar yaron ta kubutar da shi, in ji rahoton.
Damisar ta ci gaba da yin kokarin ganin ta cinye yaron, har sai da mazauna kauyen suka ji karar mahaifiyar suka kawo mata dauki, abun da ya sa damisar ta gudu zuwa daji.
Rahotannin sun kuma nuna cewa, an kwantar da mahaifiyar a asibiti kuma ba ta cikin mummunan hali, haka shima yaron yana samun kulawar lafiya.
Mahaifiyar dai ta samu matsala a hunhunta bayan ta samu rauni a cikinta, yayinda shi kuma yaron ya samu kakkarjewa a kansa.
Jaridar THE TIMES ta India ta ce, ana kan yin bincike domin dawo da damisar wajen da ake killace su, sannan kuma an umarci mazauna kauyen da su dena fitowa waje da daddare.
A na dai samun karuwar wadanda suke rasa rayukansu ta hanyar harin namun daji a India, inda alkaluman gwamnatin kasar ya nuna cewa, a tsakanin shekarar 2014 da 2019, mutane 225 ne damisa ta kashe a kasar, yayinda su kuma mutane suka damisar sama da guda 200.
Kasar India dai na dauke da kaso 70 cikin 100 na damisoshin duniya gaba daya, abun da ya nuna cewa a kasar akwai damisa har guda 2,967 a kididdigar shekarar 2018.
AFP