For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Watanni Uku Kenan Ba Tare Da Biyan ‘Yan Npower Alawus Din Su Ba

A watanni uku da suka gabata ne Jaridar Rariya ta wallafa cewa hukumar dake kula da shirin Npower za ta na biyan kudin alawus ga masu cin gajiyar shirin a dukka ranar ashirin da biyar na kowane wata.

Sai dai kuma hukumar ta yi shakulatun bangaro da masu aikin, inda suka kwashe tsawon watanni uku ba tare da biyan su hakkokin su kamar yadda ta alkawarta ba.

Jaridar JakadiyaPress ta jiyo wasu daga cikin masu cin gajiyar shirin na ikirarin gudanar da zanzangar lumana kan rashin biyan su akan lokaci, inda wasu kuma ke ikirarin dena fita wajen aiki sakamakon rashin cika musu alkawari.

Yayin da wasu ke zargin ko an dakatar da shirin ne zuwa wani lokaci, wasu kuma basussuka suka ci da zimmar za su biya idan an biyasu inda ta kai suna wasan buya da masu bin su basussukan.

Ya zuwa yanzu ba a samu wata magana daga hukumar ba wadda ke nuni da dalilin da yasa aka tsinci kai a halin da ake ciki.

Comments
Loading...