For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Waɗansu Mutane Sun Yi Wa Matar Aure Yankan Rago Bayan Sun Yi Mata Fyaɗe A Jigawa

Daga: Bala Ibrahim

Waɗansu mutane da ba a san su ba sun yi wa wata matar aure mai suna Ummi Garba ƴar shekara 26 fyaɗe sannan sukai mata yankan rago a Hadejia da ke Jihar Jigawa.

Wani mazaunin unguwar da abun ya faru, ya faɗawa wakilinmu cewa, lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata a unguwar Warwadi da ke garin Hadejia.

Ya ce, abun rashin imanin ya faru ne yayinda masu aikata laifin sukai amfani da rashin mijin matar a gida suka shiga sukai mata fyaɗe tare da yankata.

Mai magana da yawun ƴansandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Yuni na shekarar 2022 da misalin ƙarfe 6 da minti 15 na yamma, lokacin da waɗansu da ba a sani ba suka shiga gidan matar aure ƴar shekara 26, mai suna Ummi Garba, a unguwar Warwadi da ke Ƙaramar Hukumar Hadejia, sukai amfani da abu mai kaifi suka yanka maƙogwaronta.

Lawan Shiisu ya ce, jami’an ƴansanda sun garzaya wajen da abun ya faru bayan sun sami labari, inda suka garzaya da matar zuwa Babban Asibitin Hadejia domin a dubata.

Ya ƙara da cewa, Ummi Garba ta rigamu gidan gaskiya a lokacin da take karɓar magani a asibitin, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Sai dai Lawan Shiisu bai tabbatar da batun an yi wa matar fyaɗe kafin a yankatan ba.

Mai magana da yawun ƴansandan ya ce, ana bincikar lamarin kuma amma matuƙar mayar da hankali wajen ganin an kama waɗanda suka aikta laifin.

Comments
Loading...